Sunday, June 7
Shadow

Allah Sarki: Kanawa Sama da Dubu 4 sun bayar da kansu dan yakar cutar Coronavirus/COVID-19 idan ta shiga jihar

Rahotanni dsga jihar Kano na cewa mutane  jihar sama da dubu 4 ne suka bayar da kansu dan yin aikin yakar Cutar Coronavirus/COVID-19 idan aka samu bulluwarta a jihar.

 

Yawan wanda suka bayar da kan nasu ya kai mutane Dubu 4,400 kamar yanda me baiwa gwamnan shawara, Salihu Tanko Yakasai ya nunar.

 

 

 

Duk da cewa cutar bata bulla a jihar Kano ba amma jihar na ta daukar matakan kariya dan ganin hakan bai kasance ba da kuma shirin kota kwana.

 

Yanzu haka jihar da hadin gwiwar Dangote na ginin gurin killace masu Coronavirus me dauke da gadaje 600.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *