fbpx
Monday, June 27
Shadow

Allah Sarki: Watanni 11 kenan da sace daliban makarantar Yawuri dake Sokoto

A yau Litinin ne ragowar ɗaliban sakandiren Yawuri a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya ke cika wata 11 a hannun ‘yan fashin daji.

A tsakiyar watan Yunin bara ne ‘yan fashin daji suka auka Kwalejin Tarayya ta Yawuri, kuma suka yi awon gaba da gwamman ɗalibai.

Sai dai kuma ‘yan fashin da suka yi garkuwa da ɗaliban sun saki dukkan mazan da ke hannunsu amma suka ci gaba da riƙe wasu ‘yan mata.

Gwamnati ba ta komai kan ceto yaranmu’

Jiya Lahadi da yamma iyayen ɗaliban sun gudanar da taro game da wannan lamari, kuma ɗaya daga cikinsu ya fada wa BBC cewa har yanzu basu debe tsammanin sake haduwa da ya’yan nasu ba.

Cikin yanayi na damuwa da takaici, daya daga cikin iyayen yace ”ana rana ana hunturu ana ruwa ana zafi yarannan na hannun barayi saboda Allah.”

Da ya ke magana kan gwamna Atiku Bagudu mahaifin ya ce ”shi Atiku Bagudu da ya yi alkawarin cewa zai kubutar da yaran gaba daya idan mun tuntube shi ta waya ma baya daukar wayarmu.”

”Ainihin wanda ya hada mu dashi wanda dashi ake zuwa daji lokacin ya nuna mana cewa ba batunmu yake ba, kuma ya kira shi ga waya ma baya dauka.” In ji mahaifin.

Akan haka ya ce suka sake zama wasu wasu iyaye, don su sake lale, kuma su samu tabbaci daga gwamnati cewa ta gaza don su daina dogara gare ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.