fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Allahu Akbar: Dan kwallo Musulmi, Idrissa yaki yadda ya saka rigar kwallo dake tallata ‘yan Luwadi da Madigo

 

Dan kwallon na ta shan yabo sosai a wajan Musulmai da turawa wanda suma sun tsani wannan dabi’ar.

 

A shekarun baya an taba samun Kanoute da shima yaki saka rigar dake tallar caca saboda ta sabawa addinin musulunci.

 

Shugaban kasar Senegal ya yabawa Idrissa.

Shugaban Senegal Macky Sall ya bayyana goyon bayansa ga ɗan wasan Paris Saint-Germain da Senegal Idrissa Gueye kan rahotannin da ke cewa ɗan ƙwallon ya ki sanya rigar wasa da ke ɗauke tutar ƴan madigo da luwaɗi.

Karanta wannan  Ngolo Kante ya amince ya koma kungiyar Al-itihad ta kasar Saudiyya

Ƴan wasa a Faransa a ƙarshen makon da ya gabata sun sanya rigar mai launin bakan-gizo domin nuna goyon baya ga masu fafutikar ƴancin ƴan madigo da luwaɗi, kamar yadda kafar yaɗa labaran France 24 ta ruwaito.

An ambato kocin PSG Mauricio Pochettino na cewa “wasu dalilai na ƙashin kai ne” ya hana wasu ƴan wasa fitowa fili.

Rahoton ya janyo wa Gueye suka da baƙin jini wanda musulmi ne. Bai ce komi ba game da rahoton.

Amma a wani sako a Twitter, shugaban Senegal Senegal Macky Sall ya ce “ya kamata a girmama addinin ɗan wasan.”

Batun ya sa Valerie Pecresse, ƴar takarar shugaban ƙasa a zaben watan da ya gabata, tana kiran a ɗauki mataki kan ɗan wasan.

Yawancin ƴan wasan Senegal musulmai ne masu riƙo da addini. Waɗanda kuma ke mu’amular jinsi ɗaya na ɓoye mu’amular.

An haramta luwaɗi da maɗigo a kasashen yammacin Afirka, laifin da za a iya ɗaure mutum shekara biyar a gidan yari da tarar sama da dala 2,500.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *