fbpx
Friday, August 12
Shadow

Allahu Akbar: Wani malamin jami’ar Gombe ya rasu a kasa mai tsarki

Kungiyar mahajjatan jihar Gombe ta bayyana mutuwar Dr. Abdulrahnan mai Gona a kasa mai tsarki yau ranar alhamia, wanda ya kasance malami a jami’ar jihar.

Kungiyar tace Abdulrahman ya kasance malami a sashen addinin musulunci kuma tace ya mutu ne bayan yayi jinya kan kankanuwar rashin lafiya.

Mai Gona ya kasance daya daga cikin mutanen da gwamnan jihar Muhammad Yahana Inuwa ya biyawa kudin hajji domin ziyartar kasa mai tsarki.

Kuma kungiyar mahajjatan ta kara da cewa za a yi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.