fbpx
Monday, August 15
Shadow

Allahu Akbar: Wata ‘yar data je aikin hajji ta rasu a kasa mai tsarki

Allah mai girma da daukaka ya dauki rayuwar wata mata mai suna Aisha Ahmad a kasa mai tsarki watau Makkah ranar laraba.

Aisha ta kasance yar karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa a Najeriya, kuma ta rasu ne bayan tayi jinya kadan kan ciwon dake damunta.

Mataimakin sakataren mahajjatan jihar Nasarawa, Idris Al Makura ne ya bayyanawa manema labarai rasuwar matar data tafi aikin hajji.

Inda yace lafiyarta kalau kafin ta bar gida Najeriya izuwa kasa mai tsarki don ibadar Allah SWT.

Leave a Reply

Your email address will not be published.