fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Allahu Akbar:A karin farko, Wani babban shehin malamin islam, Inyamuri zai kaddamar da Qur’ani da ya fassara zuwa Inyamuranci

Babban shehin malamin addinin islama kuma Inyamuri, Mal. Muhammed Muritala Chukwuemeka zai kaddamar da Qur’ani da ya fassara zuwa yaran Inyamuranci.

 

A hirarsa da Daily Trust, ya bayyana cewa ya kwashe shekaru 5 yana fassara qur’anin kamin yayi nasara.

 

Yace kuma yayi hakanne dan taimakawa kabilarsa ta inyamurai fahimtar musulunci.

 

Yace ranar Juma’a zai kaddamar da Qur’anin da ya fassara inda yace yana kiran ‘yan uwa da abokan arziki da su halarci wajan kaddamarwar.

 

Marigayi, Shaikh Ahmad Gumi ne dai ya fara fassara Qur’ani zuwa Harshen Hausa a Najeriya.

Karanta wannan  Mutane miliyan daya muka kashe domin a samu zaman lafiya a Najeriya, cewar shugaba Buhari

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.