Jihar Kaduna ta bayyana cewa Almajirai 35,000 ne ta mayar zuwa garuruwansu na Asali inda ita kuma aka mayar mata da sama da Dubu 1.
Kwamishiniyar jin kai da walwalar jama’a ta jihar Hajiya Hafsat Baba ce ya bayyana haka ga manema labarai inda tace jihar ta mayar da Almajirai Dubu 35 zuwa jihohinsu na asali 17 da kuma wasu kasashe Makwabta.
Tace jihar Kaduna kuma an maido mata da Almajirai dama da Dubu 1. Tace wannan matakine na ganin cewa yaran un samu ilimin addini dana Boko a gaban iyayensu.
Tace da taimakon ofishin kula da yara na majalisar dinkin Duniya, UNICEF, Jihar na baiwa Almajiran da aka dawo mata dasu kulawar data kamata.
Ta bayyana cewa banda cutar Coronavirus/COVID-19 akwai kuma ciwukan dake damun wasu almajiran wanda suke so su basu kulawa kamin su mikasu ga iyalansu.