Al’ummar dake babban birnin jihar Taraba , wato Jalingo na tsaka mai wuya kan hare haren da ‘yan bindiga ke kai masu akai akai.
Inda a ranar laraba da daddare suka kaiwa wani mutun hari a yankin Lassanda dake Jalingon inda kuma suka kaiwa wani likita hari shima a gidansa.
Kuma ‘yan Vigilanti guda biyu sun kawo masu dauki amma ‘yan bindigar sun harbe su har lahira.
Wanda hakan yasa mutanen dake Jalingon keta korafe korafe kan matsalar tsaron da suke fama dashi.