Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN reshen jihar Kaduna ta caccaki ministan Sufuri, Rotimi Amaechi kan neman takarar shugaban kasa daya fito.
Ta yi caccakar ne lura da cewa, har yanzu wanda aka yi garkuwa dasu daga jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja suna hannun ‘yan Bindiga ba’a kubutar dasu ba.
Yanzu dai an kwashe kwanaki 30 kenan da yin wannan garkuwa wadda aka yi ranar 28 ga watan Maris da ya gabata.
Fasinjoji 8 ne aka kashe a harin inda wasu da dama kuma aka yi garkuwa dasu.
Shugaban CAN a Kaduna, Rev Joseph John Hayab ne ya fitar da sanarwar ranar Alhamis inda yayi kira ga gwamnati data kubutar da wadanda aka sace din.