Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya kai ziyara jihar Jigawa a ci gaba da tuntuba da yake kan tsayawarsa takarar shugaban kasa a 2023.
Ministan ya kai ziyara fadar me martaba sarkin dutse, Dr. Nuhu Muhammad Sanusi tare da tawagar magoya bayansa.
Hakanan ya gana da Gwamna Badaru na jihar Jigawan amma gwamnan bai fitar da sanarwa a hukumance kan matsayinsa na takarar Amaechin ba.
Shi kuwa sarki Dr. Nuhu Muhammad Sanusi ya bayyana Amaechi a matsayin wanda ya cancanci zama shugaban Najeriya.