Ambaliyar ruwa ta sanya akalla mutane 1,000 sun rasa matsuguni a cikin yankuna hudu da ke karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Mista Arinze Awogu ne, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Awka ranar Litinin.
Awogu ya kuma ce ambaliyar ta mamaye gonaki da dama a yankin.