Friday, July 12
Shadow

Amfanin kanunfari ga budurwa

Kanumfari yana da matukar Amfani ga Budurwa dama sauran mata gaba daya.

Da farko dai ana amfani da Kanunfari wajan magance matsalar ciwon mara da sauran ciwukan da ake ji a lokacin Al’adar mata.

Hakanan Kanunfari yana kuma taimakawa sosai wajan magance matsalar ciwon daji na mama, watau Breast cancer da mata ke fama dashi.

Hakanan Kanunfari yana maganin kurajen fuska sosai. Yana kuma hana tattarewar fata yanda fata zata zama kamar ta matashiya.

Hakanan Mata na iya amfani da Kanunfari wajan karawa kansu ni’ima da kuma samun gamsuwa yayin jima’i.

Yanda mata zasu hada Kanumfari dan amfaninsu:

Dan Magance matsalar ciwon mara da sauransu lokacin al’ada, mata na iya hada shayin Kanunfari a rika sha kadan-kadan.

Karanta Wannan  Amfanin shan ruwan kanunfari ga maza

Hakanan dan magance matsalar kurajen fuska ko magance matsalar tattarewar Fuska, ko samun fuska ta rika sheki kamar ta matashiya, ana iya sayen man shafawa da aka hada da Kanunfari ko kuma a saka Kanunfarin cikin hadin man da ake yi a gida.

Hakanan shan ruwan Kanunfari yana taimakawa mata magance matsalar Kansar Mama da sauran amfani.

Ana kuma iya hada man Kanunfari dan rika shafawa.

Ana iya rika kuskure baki da ruwan Kanunfari safe da yamma dan magance matsalar warin baki ko tsaftace bakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *