Saturday, July 20
Shadow

Amfanin lemon tsami a gashi

Lemun tsami yana da amfani mai yawa ga gashi.

Ga wasu daga cikin amfaninsa:

  1. Kawar da Amosanin Kai: Lemun tsami na dauke da sinadarin anti-fungal da anti-bacterial wanda yake taimakawa wajen kawar da Dandruff/Amosani da sauran cututtukan fatar kai.
  2. Inganta Tsawon Gashi: Ruwan lemon tsami na taimakawa wajen kara yawan jini a fata, wanda zai iya bunkasa saurin tsawon gashi.
  3. Kare Gashi Daga Faduwa: Sinadarin Vitamin C dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen karfafa gashi da kuma hana faduwar gashi.
  4. Inganta Sheki da Lafiyar Gashi: Acid din citric dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen cire datti da mai daga gashi, yana barin gashi mai tsabta da kuma sheki.
  5. Rage Yawan Mai a Gashi: Idan kina da gashi me yawan fitar da maski, lemon tsami na taimakawa wajen rage yawan mai da ke fitowa daga fatar kai da kuma gashi.
  6. Cire launin Gashi: Idan an mayar da gashin kai zuwa wata kala ta daban wanda ba baki ba kuma ana son a dawo dashi zuwa kalar baki, ana iya amfani da ruwan lemun tsami.
  7. Kawar da Cututtuka: Lemun tsami yana dauke da sinadarin antiseptic wanda yake taimakawa wajen kare gashi daga cututtuka da kuma kare fatar kai daga kamuwa da cuta.
Karanta Wannan  Amfanin lemun tsami a fuska

Hanyoyin Amfani da Lemun Tsami a Gashi:

  1. Ruwan Lemon Tsami da Ruwa: Ki hada ruwan lemon tsami da ruwa a cikin ratio na 1:2, sannan ki shafa a fatar kai da kuma gashi. Ki bar shi na tsawon minti 20 kafin ki wanke da shamfo.
  2. Ruwan Lemon Tsami da Zuma: Ki hada ruwan lemon tsami da zuma domin yin mask din gashi. Wannan hadin zai taimaka wajen karawa gashi laushi da kuma sheki.
  3. Ruwan Lemon Tsami da Man Zaitun: Ki hada ruwan lemon tsami da man zaitun sannan ki shafa a fatar kai. Wannan zai taimaka wajen rage faduwar gashi da kuma karfafa gashi.
Karanta Wannan  Amfanin lemon tsami a gaban mace

A kula, idan kina da fata mai laushi sosai wadda zata iya yin reaction cikin sauki ko kuma gashi mai laushi, yana da kyau ki dinga yin amfani da lemon tsami a hankali domin kada ya sa fata ko gashi ya yi tsauri ko kuma ya bushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *