Sunday, July 21
Shadow

Amfanin man kwakwa a gashi

Man kwakwa yana da fa’idodi masu yawa ga gashi.

Ga wasu daga cikin amfaninsa:

 1. Inganta Lafiyar Fatar Kai: Man kwakwa na dauke da sinadarai masu kashe kwayoyin cuta da kuma fungi, wanda zai iya taimakawa wajen magance dandruff/Amosanin kai da sauran matsalolin fatar kai.
 2. Karfafa Gashi: Man kwakwa yana taimakawa wajen karfafa gashi daga tushe, yana kuma rage faduwar gashi. Yana da sinadarai na lauric acid wanda ke shiga cikin asalin gashi don karfafa shi.
 3. Kara Laushi da Sheki: Yin amfani da man kwakwa yana taimakawa wajen kara laushi da sheki ga gashi, yana kuma kiyaye danshi don hana bushewa.
 4. Gyaran Karyayyen Gashi: Man kwakwa yana taimakawa wajen gyaran karyayyen gashi da kuma hana karin karyewa saboda yana dauke da sinadarai masu gyara kuma yana rufe karyayyun kan gashi.
 5. Rage Tsananin nadewar: Idan kina da gashi mai tsananin nadewa da kin mikewa, man kwakwa na taimakawa wajen sassauta gashi da kuma rage tsananin nadewa inda zaki ya mike saboda yana kara danshi a cikin gashi.
 6. Kare Gashi daga Lalacewa: Man kwakwa yana samar da wani kariya da zai rufe gashi wanda ke kare shi daga tasirin rana, iska, da sauran abubuwan da ke lalata gashi.
 7. Inganta Tsawon Gashi: Yana taimakawa wajen bunkasa saurin tsawon gashi saboda yana kara lafiyar fatar kai da kuma rage faduwar gashi.
Karanta Wannan  Ruwan kwakwa da zuma ga budurwa

Hanyoyin Amfani da Man Kwakwa a Gashi

 1. A dumamashi a wuta: Ki dumama man kwakwa sannan ki shafa a fatar kai da gashi. Ki bar shi na tsawon awa daya ko kuma ki shafa a yayin da kika zo kwanciya kafin ki wanke da shamfu.
 2. Deep Conditioning: Ki shafa man kwakwa a gashinki bayan wanka, ki bar shi na tsawon minti 30 kafin ki wanke. Wannan zai taimaka wajen kara laushi da sheki.
 3. Daily Moisturizer: Zaki iya amfani da man kwakwa kadan a kullum don shafawa a gefen gashi ko kuma a dukkan gashin don kara danshi da kuma sassauta gashi.
 4. Scalp Massage: Ki shafa man kwakwa a fatar kai sannan ki yi tausa na tsawon minti 10-15 don taimakawa wajen karfafa jini a fatar kai da kuma karfafa gashi.
Karanta Wannan  Yadda ake lemun kwakwa

Kula

 • Yana da kyau ki tabbatar da cewa kin saya man kwakwa mai tsafta wanda ba’a hadashi da komai ba kuma mara sinadarai don samun cikakkiyar fa’ida.
 • Idan kina da gashi me mai, ki yi amfani da man kwakwa a hankali don kada ya yi nauyi ko kuma ya sa gashin ya yi mai sosai.

Man kwakwa yana da tasiri mai kyau ga gashi idan ana amfani da shi yadda ya kamata kuma daidai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *