Sunday, July 21
Shadow

Amfanin man zaitun ga azzakari

Ana alakanta cewa, shafa man zaitun akan mazakuta ko Azzakari yana kara masa girma, saidai a likitance babu wani bincike da ya tabbatar da hakan.

Hakanan ana yada cewa, hada man zaitun da albasa yana kara girman azzakari amma shima wannan babu wata hujjar bincike ta masana da suka tabbatar da hakan.

Saidai kuma babu wata illa a amfani da man zaitun akan azzakari da masana suka tabbatar, dan haka zaka iya gwadawa a gani ko zai yi aiki.

Wani abu da mutane da yawa basu sani ba shine, Yawancin maza azzakarinsu ba karami bane, mutum ne da kanshi zai rika jin kamar bai gamsu da girman azzakarinshi ba har daga nan ya fara neman maganin karin girmansa.

Karanta Wannan  Maganin kara tsawon azzakari

Masana sun bayar da shawarar cewa, yana da kyau mutum yayi magana da matarsa yaji shin yana gamsar da ita a yayin jima’i? Idan dai mutum na gamsar da matarsa yayin jima’i to babu wani amfanin neman maganin karin girman Azzakari.

Hakanan ana amfani da man zaitun ga mace wadda bata da ruwan gaba yayin jima’i wanda yana taimakawa wajan jin dadin jima’i.

Saidai shima wannan yana saka fashewar kondom idan aka shafashi a gaban mace. Amma ana iya shafa man zaitun a gaban mace awa daya kamin jima’i dan karin jin dadi musamman ga wadda bata da ruwan gaba.

Hakanan wasu bayanai sun ce shafa man zaitun akan azzakari yana taimakawa azzakarin mikewa da wuri da kuma jin dadin jima’i.

Karanta Wannan  Amfanin tsotsar farjin mace

Hakanan a wani kaulin an ruwaito cewa shafa man zaitun akan azzakari yana sawa mutum ya dade yana jima’i ba tare da ya kawo ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *