Friday, July 12
Shadow

Amfanin tafarnuwa da zuma

Tafarnuwa da zuma na da matukar amfani ga lafiyar dan adam,ana iya amfani dasu tare ko daban-daban, duka zasu bayar da sakamakon da ake bukata.

Ga amfaninsu kamar haka:

Tafarnuwa na da matukar amfani wajan bayar da garkuwa akan ciwon zuciya da shanyewar rabin jiki.

Binciken masana da yawa ya tabbatar da hakan inda take taimakawa wajan gudanar da jini yanda ya kamata da kuma magance matsalar da ka iya shafar jinin.

Kara kaifin kwakwalwa da Kawar da matsalolin tsufa:

Duka zuma da tafarnuwa suna da matukar amfani wajan taimakawa mutane kaucewa cutar mantuwa musamman ga wanda suka fara manyanta.

Karanta Wannan  Amfanin man zaitun da tafarnuwa

Hakanan tafarnuwa musamman wadda ta dade a ajiye na da wasu sinadarai wanda ke taimakawa kara kaifin kwawalwa sosai da kaucewa cutar mantuwa da sauran matsalolin tsufa.

Zuma tana maganin mura:

Wani bincike na musamman ya tabbatar da zuma tana maganin kwayoyin cutar dake kawo mura. Binciken yace zumar na maganin mura kamar yanda kwayar maganin turawa ko ta likita ke yi.

Hadin Zuma da Tafarnuwa yana maganin cutukan Bacteria:

Hadin zuma da tafarnuwa na maganin cutukan Bacteria dake kawo cutar nimoniya da sauran cutukan da suka shafi sanyi.

A wani bincike da masana suka yi,sakamakon ya tabbatar da cewa hadin zumar da tafarnuwa na maganin wasu cutuka na Bacteria wanda ko maganin likita baya iya irin wannan magani.

Karanta Wannan  Amfanin man zaitun da tafarnuwa

Hakanan ana iya amfani da zuma ita kadai zata bayar da wannan sakamako, kuma ana iya amfani da tafarnuwa ita kadai itama zata bayar da wannan magani.

Saidai masana sun ce a hada su a yi amfani dasu tare ya fi bayar da sakamako me kyau.

Gargadi:

Masana sunce kada a sake a baiwa karamin yaro dake kasa da shekara 1 zuma koda kuwa lasace kawai saboda zata iya illatashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *