Attajirin dan kasuwa a Kano,Alhaji Aminu Dogo Dantata ya bayar da gudummuwar Naira Miliyan 300 ga gwamnatin jihar dan ta yaki cutar Coronavirus/COVID-19.
Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin neman tallafin yaki da cutar ta Coronavirus/COVID-19 dan samun abinda za’a tallafawa marasa karfi dashi.
FLASH, Alhaji Aminu Dantata, a businessman and an elder statesman donates N300 million to Kano State Government, a contribution to the Kano State #COVID19 Support, a gov’t committee that will provide relief materials to most vulnerable in Kano during the crisis of this pandemic.
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) March 30, 2020
Kuma tuni masu kudi da kamfanoni suka fara bayar da hadin kai kan wannan lamari.
Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya bayyana wannan kudi da Dantata ya bayar.