Shararren darektan Kannywood dake shirya fim din labarina, Aminu Saira ya bayyana cewa kwanan nan zasu cigaba da haska shirin.
Inda yace suna nan suna cigaba da daukar shirin kuma zasu fara haska shi a tsakiyar wata mai zuwa na Augusta.
Inda yace yana bawa dumbin masoyansu hakuri bisa jinkirin da suke yi da kuma hakuri.