fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Amma Rarara ya rainawa Talakawa wayau, da wanne zasu ji?>>Hakeem Baba Ahmad

Dan siyasa kuma Me fada Aji a jihar Kaduna, Hakeem Baba Ahmad yayi martani akan neman da mawakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  watau Dauda Kahutu, Rarara yayi na a tara masa Dubu-Dubu yayi waka.

 

A wani Rubutu da yayi a shafinsa na Faceboon, Hakeem ya bayyana cewa rara ya rainawa Talakawa wayau inda yace a halin matsin da ake ciki shin da wanne zasu ji?

 

Ga dai cikakken abinda ya rubuta:

 

“Kai jamaa, amma gaskiya Rarara ya raina wa talaka wayau.Wai duk kudin da yayi ta samu sanadin Shugaba Buhari, yanzu sai talakawan da ke cikin mummmunan matsi, kuma masu son Buhari sun biya shi Naira dubu-dubu sannan ya rera masu sabon wakar yabon Buhari.Idan kuma basu biya ba, ba zai yabi Buharin ba ke nan.
A karshe dai kila wata dabara ce kawai ya shirya ta kara tatsar manyan kudade daga hanyar Shugaban Kasa amma a ce talakawa ne suka tara masa, saboda kada a ji kunya a ce talaka bai tara masa kudin yabon Buhari ba.
To yanzu talaka ya ji da wanne?Yaudarar maroki, ko wahalar wannan zamani? Allah Ka yi mana abin da ba zamu iya ba.”

Kai jamaa, amma gaskiya Rarara ya raina wa talaka wayau.Wai duk kudin da yayi ta samu sanadin Shugaba Buhari, yanzu sai…

Posted by Hakeem Baba-Ahmed on Friday, September 11, 2020

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.