fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Amurka ta hana wasu ‘yan Siyasar Najeriya shiga kasarta saboda katsalandan a zabe

Kasar Amurka ta sanar da kakabawa wasu ‘yan siyasar Najeriya shiga kasar ta saboda hannu da suke dashi a yunkurin dagula harkar zabukan da aka yi ajihohin Bayelsa da Kogi a shekarar 2019.

 

Hakanan kasar ta Amurka ta kuma bana wasu ‘yan siyasar da suke kokarin aikata ba daidai ba a zabukan jihohin Edo da Ondo da ake shirin yi shiga kasartata.

Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin sakataren harkokin kasashen waje na kasar Amurkar, Mike Pempeo ta hannun kakakin ma’aikatar, Morgan Ortagus.

 

Yace a watan Yuli na shekarar 2019 kasar Amurka ta hana wasu mutane da suka aikata ba daidai ba a zabukan watannin Fabrairu da Maris na shekarar 2019. A wannan karin ma suna kara saka sunayen wanda suka hana shiga kasarsu saboda katsalandan a harkar zabe.

Karanta wannan  Kungiyar magoya bayan Tinubu ta bayar da shawarar ya dauki Gwamna Elrufai a matsayin mataimakinsa

 

Yace sun dauki wannan mataki me dan karfafa dimokradiyya a Najeriya da kuma kare muradin mutanen kasar, saisai Amurka bata bayyana sunayen wadanda ta hana shiga kasar tata ba.

 

Amma dai tace hanin akan wasu tsirarune be shafi duka ‘yan Najeriya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.