Jiyane uwargidan shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari taje garin Daura inda ta raba kayan sana’o’i ga matasa guda dari biyar, a cikin kayan sana’o’in data raba akwai keke Napep/a daidaita sahu/’yar kurkura ko kuma agwagwa da buje, kamar yanda ake kiranta a jihohi daban-daban, Hajiya A’isha Buhari ta shiga cikin daya daga cikin keken data bayar tallafi kuma an tukata.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bayan da hoton ya watsu a shadukan sada zumunta da muhawara, sai da yawa aka rika alakantashi da cewa, lokacin siyasa yayi shiyasa matar shufaban kasar tayi irin wannam abu dan a yabeta, ko kuma a kara zabar mijinta a matsayin shugaban kasa.
Wasu kuwa sun bayyana cewa zancen ba haka yakeba, kawaidai, kamar kowane shugabane, idan yaje kaddamar da wani aiki, musamman irin wannan, yakan shiga ayi dashi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});