Shugaban jami’ar Afe Babalola, watau Afe Babalola din da kansa ya bayar da shawarar daga zaben shekarar 2023.
Yace kamata yayi a daga zaben a kuma kafa gwamnatin rikon kwarya ta watanni 6 ta samar da sabon kundin tsarin mulki da za’a yi amfani dashi wajan yin zabe.
Yace dalili kuwa shine idan aka yi amfani da wannan kudin tsarin mulkin da ake dashi a yanzu, to ko da an yi zabe, ba lallai a ga wani canji a al’amuran Najeriya ba.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gayyaceshi.