fbpx
Monday, May 23
Shadow

An bai wa Messi jakadan fannin yawon buɗe idanu a Saudiyya

Ministan yawon bude idanu da shakatawa na Saudiyya, Ahmed Al-Khateeb, ya sanar da cewa fitattaccen dan wasan kwallon kafar nan a duniya Loinel Messi, ya zama jakadan yawon bude idanu da shakatawa na kasar.

Messi ya samu kyakkyawar tarba a lokacin da ya isa filin jirgin saman Sarki Abdulziz da ke Jidda a ranar Litinin.

Dan wasan kwallon kafar ya samu rakiyar takwaransa Leonardo Paredes, dan waasan tsakiya na kungiyar Paris Saint-Germain da sauran abokansa.

Da yake maraba da zuwan Messi, a shafinsa na tuwita, ministan yawon bude idanun ya ce, “A yau muna maraba da zuwan Lionel Messi da abokansa zuwa Saudiyya.

Muna taya ka murnar cewa za ka ga dumbin dukiyar da ke jibge a Bahar Maliya da kuma kayayyakin tarihin da ke kasarmu.

Karanta wannan  Dakarun Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Babbar Nasara Akan ‘Yan Boko Haram

Ba wannan ne zuwansa na farko ba, kuma ba shi ne na karshe ba, sannan ina farin cikin sanar da cewa a yanzu Messi ya zama jakadan yawon bude idanu da shakatawa a ma’aikatar yawon bude idanu ta Saudiyya.”

Wanann ne dai karo na hudu da Messi ya kai ziyara Saudiyya bayan da ya jagoranci kasarsa a wani wasan sada zumunta da kasarsa da buga da Saudi Arabia wanda aka buga a filin wasa na sarki Fahd da ke Riyadh da aka yi a 2011.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.