fbpx
Monday, August 15
Shadow

An baiwa Buhari shawarar yayi amfani da kudaden da yake kashewa kansa wajen tafiye-tafiye da wanda yake kashewa majalisar tarayya wajan biyawa ASUU bukatunsu

Kungiyar dake saka ido kan yanda ake gudanar da gwamnati ta SERAP ta baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawarar yayi amfani da kudaden da yake kashewa kansa da majalisar tarayya da sauransu wajan biyawa ASUU bukatunsu.

 

Kungiyar tace akwai Biliyan 3.6 da shugaban ya warewa kansa na tafiye-tafiye da kuma biliyan 134 da aka warewa majalisa.

 

Tace ayi amfani da wadanan kudade wajan biyawa ASUU bukatunta.

 

SERAP tace shugaba Buhari ya gaggauta mikawa majalisar tarayya da bukatar wannan canje-canje a kasafin kudin kasar.

Karanta wannan  Siyasa: Atiku ya aurar da yarinyar Sule Lamido ga jigon APC a jihar Zamfara

 

Kungiyar tace rashin biyawa ASUU bukatunsu yasa ‘ya’yan talakawa na gida a zaune yayin da ‘ya’yan masu hannu da shuni da manyan ‘yan siyasa ke ci gaba da karatu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.