Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawarar kulle hukukomin yaki da rashawa na EFCC da ICPC.
Wike ya bayyana hakane a jihar Kano yayin da yake ganawa da wakilan PDP dan neman kuri’arsu a zaben fidda gwani na jam’iyyar ta PDP da za’a yi nan gaba.
Wike yacw shugaba Buhari ya yafewa tsaffin gwamnonin Taraba da Filato laifukan satar kudin talakawa ne saboda zaben shekarar 2023.
Yace amma abinda yayin, ya kunyata hukumomin yaki da rashawa na EFCC da ICPC, musamman idan aka lura da yanda suka kai wadannan tsaffin gwamnonin kotu suka kuma tabbatar an hukuntasu.
Yace idan dai ba da gaske shugaba Buhari ke yi wajan yaki da rashawa da cin hanci ba, ya kamata ya kulle wadannan hukumomin.