Bola Tinubu ya bayyana cewa, yana girmama duka addinan da ake dasu na Musulunci da kiristanci.
Ya kara da cewa amma ya zabi musulmi a matsayin mataikainsa dan cancantane.
Ya bayyana cewa, bai kamata a bari bangaranci da addini su rika yiwa harkar siyasa katsalandan ba.
Ya bayyana cewa, idan aka zabeshi, zai yi abinda ya kamata dan ciyar da Najariya gaba.