Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO tace an bar Najeriya da sauran wasu kasashen Afrika a baya sosai wajan rigakafin cutar coronavirus.
Kungiyar tace kaso 18.7 ne cikin 100 na ‘yan Africa akawa rigakafin Allurar.
Wakilin kungiyar, Dr. Matshidiso Moeti ne ya bayyana haka a ranar Talata inda yace duk da kariyar da rigakafin ke bayarwa amma akwai Miliyoyin ‘yan Africa dake gudunta.