fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

An bayar da umurnin fille kan tauraruwar fina-finan Indiya, Deepika saboda fitowa da tayi a wani shirin fim

Hoton Deepika Padukone, 'yar fim din kasar Indiya-AP

An dakatar da fitar da wani shirin fim a kasar Indiya da mutanen kasar ke ta dakon fitowarshi, wanda shahararriyar jarumar nan, Deepika ta fito a ciki me suna Padmavati, dalilin tsayar dafitar da wannan fim din kuwa shine wani babban dan siyasar kasar ya saka ladar zunzurutun kudi dalar Amurka miliyan daya da dubu dari biyar ga duk wanda ya ciro mai kan Deepika da wanda ya bayar da umarnin shirin ya kawo mai saboda fitowar da tayi a cikin shirin fim din wanda suke ganin an wulakanta wani babban shugaban addininsu na Hindu a ciki.
Itadai wannan sarauniyar addinin Hindu me sun Padmini wadda Deepika ta taka rawa a cikin fim din a matsayinta, masu bin addinin sunce anci mutuncinta ta hanyar yanda aka nuna cewa wai tayi soyayya da wani sarkin musulmi dan kama guri zauna da kuma an nuna tsiraicinta, ta hanyar saka rigar dake nuna cibiya da Deepikan tayi a cikin shirin fim din.

Yanzu haka dai gwamnan jihar da Deepikan da iyayenta ke ciki ya bayar da umarnin basu tsaro na musamman dan kariya daga harin da za’a iya kawo musu, kuma wanda ya bayar da umarnin fim din da dan siyasar ya bayar da umarnin ciro kanshi tare dana Deepikan wanda ake kira da Sanjay Leela Bhansali yace wannan shirin fim din beci mutuncin kowaba kuma be nuna soyayya tsakanin sarayniyar da sarkin mussulmiba.

Karanta wannan  Shine mene ne hukuncin dandana abinci ga mai zumi?

Jam’iyya me mulkin kasar Indiya wadda dan siyasar daya bayar da ladar ciro kawunan masu shirin fim din ya fito daga cikinta sun nesanta kansu da wannan mummunar aniya tashi, haka kuma wani minista yayi kira da cewa a cire guraren da ake kace-nace akansu na cikin fim din kamin a sakeshi a kasuwa.

Amma dan siyasar daya saka ladar ciro da kan Deepikar da wasu mabiya addinin na Hindu masu tsatstsauran sunce sam ba zasu bari a fitar da wannan fim ba kuma ko an fitar dashi saga gidan kallon da zai nunashi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yanzu hakadai matasa ‘yan Himdun sun fara tashe-fashe da kone-konen gidajen kallo a wasu sassa na kasar Indiyar, kuma wanda ya shirya fim din ya tsayar da fitar dashi har sai yanda hali yayi.

Amma Deepikar tace hukumar kula da finafinan kasar Indiyarce kawai zata musu hukunci su yarda, kamar yanda kafar watsa labarai ta washingtonpost ta ruwaito.

Duba kaga bidiyon tallar fim din anan kasa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *