Sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban kasar,Muhammadu Buhari ya tabbatar a jiya, ya bayyana cewa, Shugaba Buhari ya zaboshine dan yana da bukatar kwarewarsa da kuma biyayya wajan samun nasara.
Da aka tambayeshi ko me ‘yan Najeriya zasu yi tsammani daga gareshi? Sai ya bayyana cewa, Basu fara ba tukuna. Sai abinda ya gani amma a sani ba mutanin Najeriya zai rika baiwa Rahoto ba, shugaba Buhari ne zai rika baiwa.
Ya kara da cewa zai yi iya kokarinsa wajan hidimtawa shugaba Buhri yanda ya kamata.
Shugaba Buhari a hukumance ya bayyana Farfesa Ibrahim Gambari a zaman majalisar zartaswa na jiya,Laraba inda kuma a wajan zaman aka yi shiru na dan wani Lokaci dan girmama tsohon ministan Shari’a, Richard Akinjide da kuma Abba kyari da suka rasu.
Farfesa Ibrahim Gambari ya taba zama wakilin Najeriya a majalisar dinkin Duniya.