Wednesday, June 3
Shadow

An bayyana lokacin da messi zai yi ritaya yayin da Barcelona suke harin dawo da Neymar daga kungiyar PSG

Tsohon dan wasan tsakiya na Barcelona Xavi yace Messi yana da damar cigaba da wasa har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa kuma yana fatan zai cigaba da buga wasan a kungiyar Barcelona har ya kai shekara ta 39.

 

 

Messi yaci dukkan wani abu da dan wasa yake da burin ci a duniyar wasan kwallon kafa tunda ya koma Barcelona daga kungiyar Newells Old boys a shekara ta 2010.
Dan wasan mai shekaru 32 yaci kyautar balloon d’Or har sau shida yayin da yafi Ronaldo da kyautar guda daya, amma sai dai bai taba lashe gasar kofin duniya ba a kasar shi ta Argentina.
Xavi yana tunanin wannan shine kadai abun da messi bai ci ba a wasannin kwallon kafa amma dan wasan yana shirin buga gasar mai zuwa wadda za’a buga a kasar Qatar shekara ta 2022.
Xavi yace Messi yanada kwararrun yan wasa biyar zuwa bakwai a tattare da shi, yayin da yake tattaunawa da Samuel Eto’o a kafar sada zumunta ta Instagram.
Kuma yana da tabbacin cewa Messi zai buga gasar a kasar Qatar saboda dan wasan yana lura da kanshi sosai kuma zai iya cigaba da buga wasannin kwallon kafa har sai ya kai shekara ta 37 ko 38 ko kuma 39 kafin yayi ritaya.
Barcelona suna harin lashe gasar la liga a wannan kakar wasan yayin da suka kasance a saman teburin gasar kuma abokan hamayyar su Madrid suna harin siyan kwararrun yan wasan, yayin da suma Barcelona suke so su dawo da Neymar daga kungiyar PSG.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *