An buƙaci masallatai da coci-coci a birnin Nairobi na ƙasar Kenya da su rage hayaniyar da masu ibada ke yi a cikinsu.
A wani sako ta shafinsa na tuwita, gwamnan Nairobi, Johnson Sakaja ya ce zai tattauna da jagororin addini kan yadda za a rage hargowar da ke fitowa daga wuraren ibadar.
A kwanan nan ne hukumomin birnin suka haramta samar da wuraren shakatawar dare a unguwannin al’umma saboda yawan hayaniya, a yanzu wasu mutanen na kiraye-kirayen ganin an aiwatar da irin wannan doka a kan wuraren ibada.
Gabanin wallafa bayanin nasa, a ranar Alhamis gwamnan ya ce ba zai bayar da umurnin rufe wuraren ibadan ba, amma zai yi ƙoƙarin tattaunawa da jagororin addinan.
Nairobi, birni ne da ke da yawan coci-coci waɗanda suka yi ƙaurin suna wurin hargowa a lokacin ibada cikin dare.