fbpx
Friday, February 26
Shadow

An bukaci Mawadata da su kasance masu tallafawa Mabukata – A cewar Shugaban gidauniyar Zakka (ZSF)

An yi kira ga MUSULMAI, musamman mawadata daga cikinsu, da su raba abin da suka mallaka ga matalauta da maƙwabta waɗanda basu da hali, domin samun rahama a wajan Allah kasancewar Sadaka wani Nau’ine na ibada kuma aiki ne na masu tsoran Allah.

Wannan nasihar ta fito ne daga wani malamin addinin musulinci, Imam Abdulfatah Abdulsalam, a garin Akure, dake jihar Ondo, yayin rabon kayan tallafi, da kuma tsabar kudi ga marassa karfi a karkashin gidauniyar Zakka da Sadaqqah Foundation (ZSF).

A cewar Imam Abdulfatah Daurewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma na samuwa ne muddin idan Mawadata su ka fidda dokiyoyin su wajan tallafawa mutanan da su ke da bukata.

Hakanan Wani bawan Allah da ya amfana da tallafin kudi mai suna Taofiqah Suleiman, ya godewa Allah tare da nuna farin cikin sa bissa hubbasa da kungiyar ke yi wajan taimakon Al’umma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *