Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya sha caccaka, musamman wajan ‘yan kudu bayan da ya baiwa wani amsa daya jawo hanlinshi kan yin wani abu akan maganar Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Yellow.
Kotu dai ta yankewa Yellow hukuncin shekaru 26 a gidan yari bayan kamashi da laifin tafiya da wata yarinya Ese Oruru a shekarar 2015, lokacin tana da shakaru 13 inda aka zargi ya canja mata addini da karfi da kuma cin zarafinta.
Wani mai suna Hammad Yusuf Saleh ya jawo hankalin Bashir inda yace ya kamata ayi wani abu akan shari’ar Yunusa saboda ba’a mai adalci ba, yayi kiran da a daukaka karan.
Bashir ya bashi amsar cewa, dan uwa bani da wani karfin da zan iyayin wani abu akan hukuncin da kotu ta yanke. Saidai zan yi kokarin ganin na tuntubi wanda nake ganin suna da karfin ko Allah zai sa a dace.
Da yawa dai, Musamman daga kudu sun yi Caaa akan Bashir inda suka zargeshi da goyawa Yunusa baya da kuma yunkurin canja hukuncin kotu.
Saidai daga baya bashir ya fito ya bayyana cewa yayi maganane ba tare da sanin cikakken yanda lamarin shari’ar Yunusa take ba amma yana Allah wadai abin.