fbpx
Monday, December 5
Shadow

An cigaba da shari’ar Maryam Sanda: Matar da ake zargi da kashe mijinta

A ranar Alhamis ne aka ci gaba da zaman shari’ar da ake yi na matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, a wata babbar kotun birnin tarayyar Najeriya, Abuja.A watan Nuwamba ne dai aka gurfanar da Maryam a gaban kotun bisa zarginta da kashe mai gidanta, Bilyaminu Bello, bayan ta daba masa kwalba a kirji.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A zaman shari’ar na ranar Alhamis, Maryam ta tsaya a gaban mai shari’ar rike da carbi a hannunta.
Sai dai alkalin ya dakatar da ci gaba da shari’ar saboda a cewarsa, sai ‘yan sanda sun kawo wasu mutum uku da ake zargi da jirkita hujjojin da za su iya taimakawa wajen gano yadda aka kashe Bilyaminu.
Wadannan mutum ukun sun hada da wata Maimuna Aliyu da Safiya Aliyu, wadanda ake kyautata zaton makusantan Maryam ne.
Sai dai ‘yan sandan sun ce ba su samu damar aikewa da mutanen sammaci ba ne, shi ya sa ba su gurfana a gaban kotun ba.
Amma alkalin ya ce bai ga wata alama da ke nuna cewa ‘yan sandan sun yi iya kokarinsu da ke nuna cewar sun aike wa da mutanen sammaci ba.
Masu shigar da karar dai sun yi alkawarin cewa za su kawo mutane ukun da ake zargi da jirkita hujjojin ranar 14 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da sauraron karar.
A wannan karon dai wani sanannen lauya mai suna JB Dawudo ne yake kare Maryam a shari’ar, kuma ya nemi alkali ya bayar da belinta zuwa ranar da za a sake zaman kotun.
Sai dai alkalin kotun Yusuf Halilu, ya yi watsi da bukatar lauyan, inda ya ki bayar da belinta, amma ya ba shi damar ganawa da ita na tsawon minti 20 kafin a wuce da ita gidan yarin Suleja.
Abokin aikinmu Abdulwasi’u Hassan, wanda ya halarci zaman kotun, ya ce Maryam ta shiga kotun dauke da jaririyarta ‘yar wata takwas wadda take ta tsala kuka.
Kazalika ya ga Maryam ta shiga motar gidan yarin da jaririyar tata karkashin rakiyar ma’aikatan gidan yari.
bbchausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Saboda Tsantsar Son Musulunci Mahaifiyar Tinubu Ta Gagara Zama A Landan A Lokacin Da Ake Jinyar Ta A Can Saboda Ba Ta Jin Kiran Sallah, Cewar Kabiru Gombe

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *