Jami’an So Safe dake jihar Ogun sun damke wani barawo bayan ya sato jar waya a cocin Deeper Life dake karamar hukumar Obafemi Owode.
Hukumar ta bayyana cewa barawon, Omotayo Oni yaso ya basu wahala a lokacin da suka tambaye shi inda ya sato wayar.
Domin ya kaisu wurare daban daban kafin yace masu a cocin Deeper Kife ya sato su.
Kuma koda sukaje cocin masu gadinta sunyi matukar mamaki yadda akayi ya tsere ba tare da sun kama shi ba.