Hukumar ‘yan sandan jihar Nasarawa sunyi nasarar damke wani kasurgumin dan Boko Haram din daya tsere a gidan kurkukun Kuje.
Dan Bokon Haram din mai suna Hassan Hassan yana daya daga cikin guda 64 da suka tsere ranar talata a harin da Boko Haram ta kaiwa gidan kurkukun.
Hankulan al’ummar Najeriya ya tashi sosai ganin cewa babban kurkukun kasar ma bai sha ba, amma abin cewa kawai shine Allah ya kawo mana saukin matsalar tsaro a Najeriya.