Inspecta janar na ‘yan sanda Usman Baba ya jinjinawa hukumar saboda namijin kokarin da take yi a kwanakin nan.
Kuma yace ba zasu laminci irin wa’yan nan lafukan da miyagun mutane ke aikatawa ba, sannan barayi ba zasu taba samun walawala ba a Najeriya.
Shugaban ‘yan sandan ya bayyana hakan ne bayan hukumar ta damke wasu ma’aikatan Banki da suka hada kai ‘yan damfar don satar naira Biliyan 3.4.
Inda yace yana jinjinawa hukumar ‘yan sanda na jihar Oyo da suka dakatar da wannan iftila’in.