Hukumar dake yaki akan safarar dan adam da kuma cin zarafi ta NAPTIP ta damke wata mata bayan ta lallasa mai aikinta har ta mutu a jihar Anambra.
Kuma tayi kokarin kai yarinyar asibiti amma ta mutu a hanyar zuwansu, wanda hakan yasa ta binne a cikin a cikin daji.
Matar ta amsa laifin data ake tuhumarta dashi kuma ta kai hukumar ta NAPTIP cikin dajin wurin data binne yarinyar har gawarta ta fara lalacewa.
Yayin da yanzu ake tsare da ita lafin a makata a gaban kotu.