fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An damke mutane hudu da ake zargin sun kashe tsohon dan sanda da wasu mutanu biyu a jihar Delta

Hukumar ‘yan sanda ta damke ‘yan damfara guda hudu watau Yahoo Boys da ake zargin sun kashe tsohon jami’in dan sanda da wasu mutane guda biyu a jihar Delta.

A ranar talata da misalin karfe bakwai na yamma ‘yan bindigar suka kai wannan harin inda suka harbi mutane uku suka mutu hadda tsohon dan sandan, David Amenkhienan.

Amma hukumar ‘yan sanda ta jihar ta bayyana cewa ta damke mutane hudu data ke zargi cewa sune suka aikata wannan bannar kuma tana cigaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published.