Wani mutun mai sun Ebute Oba a jihar Anambra ya kashe wata mata mai yara biyu sakamkon fadan da sukayi a tsakaninsu.
Hukumar ‘yan sanda ta damke mutumin daya aikata wannan laifin na kashe matar mai suna Uzoamaka Ekpe mahaifiyar yara guda biyu.
Hukumar tace ya kashe tane bayan ya nausheta a kirjinta yayin da suke fada, wanda hakan yasa ta suma aka kaita asibiti wa’adinta ya cika a can.