fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An damke wani matashi dan jihar Gombe dake aikata lalata da kanwarsa ‘yar shekara 12

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta jihar Gombe tayi nasarar kama wani matashi dan shekra 35, Abubakar Hamidu wanda ya yiwa kanwarsa ‘yar shekara 12 fyade.

Mai magana da yawun hukumar, Muhid Abubakar ne ya bayyana hakan a yau ranar juma’a, inda ya kara da cewa wannan lamarin ya faru ne a kwatas din Jauro Abare.

Inda yace sun kama shine bayan wani mutun Muhammad Hamza dake kwatas din kasuwar Mata ya kawo masu wannan korafin, inda yace sau biyu yayi lalatar da knwar tasa.

Mai magana da yawun hukumar yace an kai yarinyar da yayan mata asibti domin ayi masu gwaje gwaje kuma da zarar an kammala zasu maka shi a kotu bayan daya amsa laifin nasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.