fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An daure wata mata a Kano data sayarwa da wani fili da takardun karya

Babbar kotun Gwamnatin tarayya dake Kano ta daure wata mata, Habiba Abubakar shekaru 7 a gidan yari bayan samunta da sayarwa wani mutun fili da yakardun karya.

 

Matar ta sayarwa da mutumin filin akan Miliyan 2.2 a Unguwar Rijiyar zaki amma daga baya wani ya zo ya ce filin nasa ne.

 

Saidai matar ta karyata wannan zargi amma shaidu sun tabbatar da zargin. Mai shari’a,  J.K Daggar ya yanke mata hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari da kuma mayarwa mutumin da ta damfara kudinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.