fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

An dawo da gwajin cutar korona a Kano

Hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce za a dawo da yin gwajin cutar korona a asibitin Malam Aminu Kano bayan rufe dakin gwajin.

Shugaban hukumar NCDC Dr Chikwe Ihekwaeazu wanda ya fitar da sanarwar a Twitter ya ce a gobe Laraba za a bude cibiyar gwaji ta biyu a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Wasu bayanai dai sun ce an dakatar da gwajin ne a Kano saboda rashin kayan aiki na yin gwajin gano masu dauke da cutar korona.

An dauki kwanaki kusan hdu, hukumar NCDC ba ta fitar da bayana ba kan cutar korona a Kano, duk da yawan mace-macen da aka samu a jihar da ake alakantawa da cutar korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published.