Shugabar masu dafawa yaran makarantun gwamnati abincin tallafi ta jihar Anambra, Mrs Eriken Uzoamaka ta bayyana cewa mutuwar masu dafa abinci goma ya dakile hanyar cigaba da ciyar da yaran.
Ta bayyana hakan ne yayin datake ganawa da manema labarai a wani taro da suka gudanar na kwanaki biyu a babban birnin Anambra, watau Awka amma bayyana abinda ya kashe ma’aikatan ba.
Inda tace ba za’a cigaba da baiwa yaran abincin ba saboda basu maye gurbin ma’aikatansu goma da suka mutu ba, kuma hakan ba karamin kalubale bane a wurin su.
Inda a karshe ta kara da cewa kuma tsadar kayan masarufi a kasar nan shima wani kalubale ne da suke fuskanta.