fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An fara aikin Shimfida Titin Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an fara aikin shimfida titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano.

 

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya tabbatar da hakan inda yace yanzu haka an fara aikin daga bangaren jihar Kaduna.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da fara aikin inda shima ya saka hotunan yanda aikin ya fara daga jihar Kaduna.

Aikin na daga cikin kokarin gwamnti na shimfida titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published.