fbpx
Thursday, May 26
Shadow

“An fitar da Yusuf Buhari zuwa kasar Jamus”>>inji The Cable

Da daya tilo gurin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, da fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa, yayi hadari da babur a daren shekaranjiya, wanda yayi sanadiyyar samun ciwo a kai ya kuma karye a kafa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rahotanni dake fito daga The Cable da safiyar yau Alhamis, sun bayyana cewa an fitar da dan shugaban kasar zuwa kasar Jamus dan cigaba da duba lafiyarshi acan, The cable ta kara da cewa an tafi da dan shugaban kasar zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe ake Abuja yayin da aka sarkafamai na’urar tallafawa numfashi.
Daga nanne aka dorashi jirgi tare da wasu likitoci da zasu rika kula dashi a cikin jirgin kafin su isa kasar Jamus din.
Muna fatan Allah ya bashi lafiya da dukkan sauran ‘yan uwa da suke gidaje da asibitoci.  


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Kalli Hotuna: Yanda wani Fasto ya baiwa mahaifan Deborah kyautar katafaren gida da mota a Fatakwal

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.