Shugaban ma’aikata Abba kyari da kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Winnifred Oyo-Ita sun sasanta sabanin da akayi rade-radin cewa sun samu a satin daya gabata, a yau dai wajan zaman majalisar zartarwa an ga ma’aikatan biyu tare suna kyalkyala dariya, wanda hakan yake nuna cewa kodai sun shirya ko kuma dama can babu wani sabani da ya shiga tsakaninsu.
A zaman majalisar zartarwa na satin daya gabatane aka ruwaito cewa ma’aikatan biyu sun yi cacar baki da juna a cikin fadar gwamnatin tarayya akan wata takar da ta fita daga ofishin Oyo-Ita wadda ya kamata ace tashiga ofishin shugaban kasane kawai amma sai gashi an same ta a gurin kafofin watsa labarai.
Takardar dai tayi bayanine akan yanda aka dauki Abdulkadir Maina aiki wanda shugaban kasane ya bukaci ayi bincike akan yanda ya dawo aiki a gwamnatinshi, kuma takardar kamar yanda kafofin watsa labarai da yawa suka wallafa, ta fallasa cewa shugaban kasar yasan da dawowar Maina aiki cikin gwamnatinshi.
Fitar wannan takardane hannun manema labarai ake saran ya haddasa cacar baki tsakanin Abba Kyarin da Oyo-Ita, wanda har aka ruwaito cewa shugaba Buharin wai ya kirasu dan yaji dalilin cacar bakin nasu, rahoton da gwamnatin tarayyar ta karyata.