Sunday, June 7
Shadow

An gano cewa na ninka yawan masu cutar Coronavirus/COVID-19>>Bincike

Rahotanni daga kasar Ingila sun gano cewa an nunka yawan gwaje-gwajen Coronavirus/COVID-19 da dama.

 

Rahoton da The Telegraph ta kasar ta ruwaito sun bayyana cewa gwaji 2 da akawa mara lafiya 1 ana kirkashi a matsayin gwaji 2.

Watau idan aka dauki samfurin miyau dana majina a jikin mutum daya to kowane gwaji ana kirgashi a matsayin gwaji 1 ne wanda hakan  ke nunka yawan sakamakon da ake samu da sama da kaso 20 cikin 100, kamar yanda Masana suka bayyana.

 

Kuma hukumar Lafiya ta kasar ta tabbatar da wannan kuskure da ake samu.

 

Kasar Ingila nada yawan masu Coronavirus/COVID-19 250,908 inda 36,042 suka rasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *