fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

An gano gawar yarinyar da ruwa ya tafi da ita a jihar ondo cikin wannan makon

An gano gawar wata yarinya da ruwa ya tafi da ita a Ikere dake karamar hukumar Akoko a jihar Ondo.

Yarinyar mai suna Motunrayo John na wasa a gefen rafi ne yayin da ake ruwa inda take gwada zurfin rafin wanda har ya kaiga ruwan ya tafi da ita.

Inda wata kawarta ta bayyana cewa sunyi kokarin ceto ta amma abin yafi karfinsu haka nan suna gani ruwan ya tafi da ita ranar talata 21 ga wannan watan.

Hukumar ‘yan sanda sun bayyana cewa an gano gawar ne bayan kwanaki uku da ruwan ya tafi da ita, kuma an mikawa iyayenta don suyi mata jana’iza.

Leave a Reply

Your email address will not be published.