Akalla gawarwakin mutane 213 ne aka samu bayan musayar wuta data faru tsakanin ‘yan Bindiga da sojojin Najariya a Jihar Zamfara.
Hakanan sojoji 10 sun rasa rayukansu a wannan kazamin artabun kamar yanda kafar PRNigeria ta ruwaito.
Lamarin ya farune a yankin Malele Dansadau inda kuma rahoton yace an kashe ‘yan Bindigar da yawa.
Sojojin sama dana kasa ne suka yi artabu da ‘yan Bindigar wanda lamarin ya kare da nasara akan ‘yan Bindigar.
Ana dai yawan samun matsalar fadan fulani da manoma a yankunan Malele, Maigoge, Yan Sawayu, Ruwan Tofa, Mai Awaki, da Zama Lafiya na jihar wanda ya mayar da yankin me matukar hadari.